Gwamnatin Bauchi ta yi amai ta lashe

Image caption Sojojin Najeriya na yunkurin samar da zaman lafiya

A jihar Bauchi dake arewacin Najeriya, gwamnatin Jihar ta janye dokar hana goyo kan babur a cikin sa'o'i ashirin da hudu da ta sa dokar.

Takaddama dai ta kunno kai a cikin sao'in da gwamnatin ta saka dokar abinda ya tilastawa gwamnatin sake fitar da sanarwa dake cewa ta fasa takaita amfani da baburan.

Wasu dai na ganin yadda gwamnatin ta yi amai ta lashe, wata alama ce karara ta rashin sanin makamar mulki.

Sai dai gwamnatin cewa take yi ba haka batun yake ba, ta sake yin la'akari ne da halin da ake ciki a Jihar.

Karin bayani