Shugaban Cyprus ya bukaci 'yan Kasar su rungumi kaddara

Taron Majalisar zartarwar Cyprus
Image caption Taron Majalisar zartarwar Cyprus

Shugaban Cyprus ya fada wa 'yan Kasar sa cewa dole ne su amince da shirin ceto tattalin arzikin Kasar ko kuma Kasar ta fuskanci durkushewar tattalin arziki.

Shugaban Cyprus ya yi jawabi ne ga 'yan kasar game da dalilin da ya sa yake goyan bayan shirin nan na ceto tattalin arzikin kasar wanda zai lashe dubban miliyoyin daloli, wanda kuma ya janyo fusatar jama'a a cikin kasar

Shirin ya hada da cire haraji na kashi goma cikin dari ga duk wani asusu na ajiya, domin rage bashin da ake bin bankuna

Shugaban yace shirin ya na da ciwo amma shine wanda yafi dacewa a daidai wannan lokaci

Karin bayani