Jam'iyyun gurguzu na taro akan Mali

Bazoum Mohamed
Image caption Jam'iyyun gurguzu har da na Mali na tattaunawa a Nijar

A Jamhuriyar Nijar kungiyar Jam'iyun siyasa masu ra'ayin gurguzu na duniya reshen Afrika ta soma wani taro da zummar kawo tata gudummuwar ga kokarin da kasashen duniya ke yi na shawo kan rikicin kasar Mali

Jam'iyar PNDS Tarayya ce mai mulki a kasar Nijar wacce mamba ce a kungiyar ta bada shawarar shirya taron.

Shugaban jam'iyyar na PNDS Tarayya ya shaidawa BBC cewa akwai jam'iyyu biyu masu ra'ayin gurguzu a Malin, a saboda haka sun gayyace su domin su tattauna hanyoyin da za'a samu ci gaba a Kasar

An kashe sojan Faransa na biyar a Mali

A wani bangaren kuma, Gwamnatin kasar Faransa ta sanar da cewa an kashe wani sojan ta daya a arewacin Mali.

Wannan shine Sojan Faransa na biyar da aka kashe tun bayan da su ka kaddamar da yaki domin fatattakar 'yan tawayen dake iko da arewacin Malin tun watan Afirilun bara, wadanda ake alakanta su da Kungiyar Alqaeda.

A cewar ma'aikatar tsaron Faransa wata katuwar nakiya ce ta fashe a karkashin motar da ke dauke da Kopur Alexendra Van Dooren ranar asabar lokacin da suke duba wuraran da 'yan tawaye ke boye makamansu a tsaunukan Ifoghas dake arewacin kasar Malin

Karin bayani