ANC ta rusa kwamitin matasa

Image caption Wasu 'yan jam'iyyar ANC

Jam'iyyar ANC mai mulkin ƙasar Afrika ta Kudu ta rusa kwamitinta na matasa, saboda abinda jam'iyyar ta kira rashin da'ar da ke fitowa daga kwamitin abinda a lokuta da dama yake jefa jam'iyyar cikin ruɗani.

Sakataren jam'iyyar, Gwede Mantashe ya ce an dakatar da shirin ɓangaren matasan na gudanar da zaben shugabanci ba tare da wani ɓata lokaci ba.

A bara ne dai aka kori tsohon shugaban matasa na jam'iyyar Julius Malema, saboda kawo saɓani a cikin jam'iyyar.

Jam'iyyar ANC mai mulkin Afurka ta kudu dai tana cigaba da fuskantar kalubale aciki da waje ANC.