Bafaranshe ya yi magana a bidiyon Boko Haram

Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar Boko Haram
Image caption Faransawan da ake garkuwa da su na cikin mawuyacin hali

Daya daga cikin Faransawan da kungiyar nan ta Jama'atu Ahlus-Sunnah Lid'da'awati wal Jihad suke garkuwa da su, ya yi wani kira ga Jakadan Kasar Faransa a Nigeria domin ganin an sake su.

Ba-Faranshen, mai suna Tanguy Moulin-Fournier, wanda ya fito a wani faifan bidiyo da kungiyar, wadda wasu ke kira Boko Haram ta fitar, yace ana rike da su a wani wuri a cikin Hamada, kuma yanayin da suke rayuwa yana da matukar wahala.

Mutumin, wanda ya bayyana kansa a matsayin Maigida na iyalan nan bakwai da kugiiyar ta Jama'atu Ahlus-sunna lid'daawati wal jihad ke garkuwa da su ya bayyana cewa abincinsu da ruwan sha na gab da karewa.

Ya ce kowane garin Allah ya waye, karfinsu na ci gaba da karewa, kuma su na fama da rashin lafiya a hamadar da ake tsare da su.

Mr. Fournier ya bayyana cewar kungiyar ita ce ta bukace shi da ya janyo hankalin Jakadan kasar Faransa a Nigeria, ga yanayin da 'ya 'yan kungiyar suke ciki, wadanda su ka hada da maza da kananan yara wadanda ake tsare da su a Nigerai da Cameroon.

Kasar Cameroon dai ta sha musanta cewar ta na rike da 'yan Kungiyar ta Jama'atu Ahlul-sunna lid da'awati wal jihad.

Ba'a dai san lokaci ko kuma wurin da aka dauki wannan faifan bidiyo ba,

Karin bayani