Matakin ceto Cyprus bai da ce ba - Putin

Shugaban kasar Russia Vladmir Putin, ya soki shirin kasashen duniya na ceto tattalin arzikin kasar Cyprus wanda zai shafi masu ajiyar kudade.

Mr Putin ya ce babu adalci a cikin shirin kuma yana da illa.

An yi kiyasin cewa kamfanoni da bankunan Rasha sun ajiye akalla dala miliyan 30 a Cyprus a karshen bara.

Fira ministan Rasha Dmitry Medvedev, ya ce kasarsa na duba martanin da za ta mayar kan shirin na sanya haraji kan masu ajiya.

Matakin dai na fuskantar adawa daga jama'ar kasar ta Cyprus, kuma majalisar dokokin kasar ta dage muhawarar da ta shirya yi kan batun a yau zuwa gobe Talata.