'Yan makaranta sun yi wa wata fyade a Amurka

Image caption 'Yan makarantar da ake zargi da fyaden sun gurfana a gaban kotu

A wata shari'a da ta tunzura mutane da dama Amurka ita ce wasu 'yan kwallo biyu 'yan babbar makaranta a jihar Ohio da aka same su da laifin yi wa wata Yarinya 'yar shekaru 16 da haihuwa fyade a lokacin da suka hadu da ita a wajen wani liyafa.

An yanke wa matasan biyu Trent Mays da Ma'Lik Richmond hukuncin akalla shekara daya a gidan Kurkuku na Yara.

Alkalin Kotun Thomas Lipps wanda ya karanta hukuncin; ya ce, "wannan Kotu ta yanke hukuncin cewar wadannan Yara sun saba wa doka, sun kuma gaza kare kansu daga dukkan laifuka uku da aka tuhume su da aikatawa."

Masu gabatar da kara sun ce yarinyar ta bugu ne da barasa ba ta ma san lokacin da suka afka ma ta ba.

Batun dai ya yadu ne ta kafofin sada zumunta da kuma hotuna da video na cin fuskar da aka rinka yadawa.

Karin bayani