An kashe mutane da dama a Kano

An kashe mutane da dama a Kano
Image caption Daga tashar ne jama'a ke zirga-zirga tsakanin Kudu da Arewacin Nigeria

Rahotanni daga jihar Kano a arewacin Najeriya na cewa akalla mutane 20 ne suka mutu bayan fashewar wasu abubuwa daban-daban a unguwar Sabon Gari.

Wadanda suka shaida lamarin sun gayawa BBC cewa fashe-fashen sun faru ne a tashar motoci ta New Road, kuma lamarin ya ritsa da motoci da dama.

Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin.

Sai dai birnin Kano da arewacin Najeriya na fama da hare-haren da a mafi yawan lokuta ake dora wa kan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram.

Karin bayani