Bosco Ntaganda ya miƙa kansa

Image caption Bosco Ntaganda

Amurka ta ce mutumin da ake zargi da aikata laifukan yaƙi Bosco Ntaganda, ya miƙa kansa ga ofishin jakadancinta da ke ƙasar Rwanda, inda ya nemi a mika shi ga kotun hukunta laifukan yaƙi ta duniya da ke birnin Hague.

Ntaganda wanda ya jagoranci tawaye a gabashin jamhuriyar Demokuradiyyar Congo yana fuskantar tuhume-tuhume a kotun duniya mai hukunta laifukan yaƙi, wadanda suka hada da ɗaukar yara aikin soji, da kisan gilla, da kuma fyade.

Ntaganda ya musanta wannan zargi.

Wakilin BBC a Washington kenan yake cewa, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Victoria Nulan, ta ce Amurkar, wacce ba mamba bace a kotun ta ICC, tana tuntuɓar sauran ƙasashen duniya ciki har da Rwanda domin ganin yadda za ta miƙa shi.