Kudiri da zai bukaci a yiwa Boko Haram ahuwa

Image caption Shugaban Kungiyar, Boko Hara, Imam Abubakar Shekau

A Najeriya, wasu 'yan majalisun dokokin kasar sun fara tunanin zartar da kudirin da zai bukaci gwamnatin kasar ta yi wa 'yan kungiyar jama'atu ahlissunannah lid da'awati wal jihad ahuwa.

A cewar 'yan majalisar ahuwar ce kawai za ta wanzar da zaman lafiya, duk kuwa da cewa shugaban kasar na dar-dari da wannan ra'ayin.

'Yan Majalisar Dokokin Najeriya da ke nema a yiwa kungiyar Boko Haram ahuwa a sannu a hankali na kara yawa duk da cewa Shugaba Goodluck Jonathan ya baya-baya ga batun ahuwan.

Senata Sahabi Ya'u ya shaidawa BBC cewa ganin rikici yaki ci yaki cinyewa kamata ya yi a yiwa kungiyar Ahuwa domin samar da zaman lafiya.

"ya kamata shugaban kasa ya koma ga tarihi ba yau aka saba ahuwa ba." In ji Senata Sahabi Ya'u.

Yan Majalisar sun ce idan yanayi ke tilasta wasu abubuwa kamar yadda gwamnatin Shugaba Umar Musa Yar'aduwa ta yiwa masu ikirarin yanta yankin Naija Delta ahuwa, toh babu laifi idan aka ari wannan dabarar.

"muna da hurumin gabatar da kudurin a gaban Majalisa, kuma muddin Shugaban Kasa bai kawo karshen wannan matsala da muke fuskanta ba, zamu dauki mataki." Senata Sahabi.