Majalisar dokokin Cyprus ta yi watsi da shirin neman ceto

Masu zanga zanga a Cyprus
Image caption Masu zanga zanga a Cyprus

Majalisar dokokin kasar Cyprus ta yi watsi da shirin samo kudaden ceto tattalin arzikinta da kasashen duniya za su bayar, wanda zai daga kafa ga masu kananan kudi na ajiya a bankuna.

Daukacin 'yan majalisar dai bakinsu ya zo daya, na kin amincewa da bashin da za a baiwa kasar.

Wani dan majalisa ya ce, "na yi ammana an lalata kimar tsarin bankunanmu, a don haka ina ganin cewar da kamar wuya a samu daidaito a wannan mawuyacin halin."

A ranar Laraba za a yi wata tattaunawar gaggawa a kan batun.

Masu bada lamuni na kasa da kasa sun hakikance a kan cewar dole ne sai kasar Cyprus ta daga kafa ga masu ajiyar kudin da bai kai Euro dubu 100 ba, a kan wannan sabon harajin inda suka ce masu hannu da shuni ne zasu biya harajin kashi 15 cikin 100.

Karin bayani