'An yaudari duniya kan yakin kasar Iraki'

An yaudari duniya kan yakin kasar Iraki
Image caption An dade ana zargin Burtaniya da Amurka da shiga yaki babu-gaira-babu dalili

Karyar da wasu jami'an leken asirin Iraki suka shirga - ita ce kasashen Burtaniya da Amurka suka dogara da ita wurin mamayar Iraki - cewa Saddam Hussein na da makaman kare dangi.

Sai dai tun kafin fara yakin, manyan bayanan sirri da aka samu sun nuna cewa bashi da su, kamar yadda shirin BBC na Panorama ya gano.

BBC ta gano cewa muhimman bayanan sirri guda biyu da aka samu wadanda za su taimaka wurin kaucewa yakin, an yi watsi da su ko kuma an yi amfani da bangaren da ake so, sannan aka yi watsi da wani.

Watanni shida kafin mamaye Iraki, Fira ministan Burtaniya na wancan lokacin Tony Blair, ya gargadi jama'ar kasarsa game da barazanar makaman kare dangin da Saddam Hussein ke da su.

"Shirin makaman na nan bai rushe su ba," a cewarsa. "Yana ci gaba da inganta su." Mr Blair ya yi amfani da bayanan sirri kan makaman wurin halatta yakin na Iraki.

A wannan ranar ce, 24 ga watan Satumban 2002, gwamnati ta wallafa takardun sirrinta wadanda aka yi ta takaddama akai kan makaman kare dangin da suka ce shugaban Iraki na wancan lokaci ya mallaka.

Gazawar bayanan sirri

Mafi yawan bayanan sirrin da gwamnatocin Burtaniya da Amurka suka dogara da su basu da tushe, tunani ne kawai da kuma karya.

Kamar yadda Janar Mike Jackson, shugaban rundunar sojin Burtaniya na wancan lokacin ya bayyana, "ana zaton wuta a makera sai ga ta a masaka", domin kuwa abinda aka zaci cewa gaskiya ne daga baya ya zama karya.

An samu wasu karin bayanan sirrin, sai dai basu da tasiri.

Lord Butler, wanda bayan yakin, ya gudanar da binciken gwamnati na farko kan batun makaman kare dangin, ya ce Mr Blair da jami'an leken asiri sun "yaudari kansu".

Sai dai Lord Butler da Sir Mike sun amince cewa Mr Blair bai yi karya ba, saboda a cewarsu ya yi imanin cewa Saddam Hussein na da makaman kare dangi.

Amma tsohon ma'aikacin hukumar leken asiri ta Amurka CIA Bill Murray bai ji dadin yadda aka yi amfani da bayanan sirrin da aka samu daga wadannan manyan jami'ai biyu ba.

"Ina ganin mun samar da bayanan sirri masu inganci kamar yadda kowa ya samar kafin yakin, wadanda dukkansu gaskiyarsu ta fito fili daga bisani.

Sai dai abin takaici dukka bayanan an yi watsi da su sannan aka ki yin amfani da su."

Karin bayani