An kai munanan hare-hare a Iraki

An kai munanan hare-hare a Iraki
Image caption Wannan ita ce rana mafi muni a kasar cikin watanni shida

Akalla mutane 48 ne aka kashe a wasu jerin hare-haren kunar bakin wake da aka kai da motoci a ciki da wajen birnin Bagadaza na kasar Iraki, a cewar jami'ai.

Harin wanda aka shirya sosai ya shafi kasuwanni, gidajen cin abinci, tashoshin mota da kuma ma'aikata a lokacin da jama'a ke yunkurin tafiya aiki da safe.

Majiyoyin 'yan sanda sun shaida wa BBC cewa fiye da mutane 150 ne suka samu raunuka a tashin hankalin na ranar Talata.

Wannan ne hari mafi muni da aka kai a kasar cikin watanni shida wanda ya zo a dai dai lokacin kasar ke cika shekaru goma da zagayowar mamayen da Amurka ta jagoranta wanda ya kifar da gwamnatin Saddam Hussein.

Gurgunta gwamnati

Tashin hankali ya ragu a Iraki tun bayan shekarun 2006 da 2007, sai dai an ci gaba da kai hare-haren bama-bamai.

Kungiyoyin masu fafutuka da ke da alaka da Al-Qaeda sun sha alwashin kai hare-hare kan mabiya darikar Shi'a da kuma jami'an gwamnati.

Fatansu shi ne na gurgunta gwamnatin kasar wacce 'yan Shi'a ke jagoranta.

A wani lamari mai kama da nuna damuwa kan halin rashin tsaro, majalisar zartarwar kasar ta dage zaben da aka shirya gudanarwa a ranar 20 ga watan Afrilu a gundumomin Anbar da Ninever sai nan da watanni shida.

Yawancin hare-haren sun shafi unguwannin da 'yan Shi'a suka fi yawa, kuma sun kunshi motocin kunar bakin wake kusan 15 da wasu bama-baman gefen hanya da kuma harbe-harben bindiga.