Obama ya yi kira ga Iran ta samawa kanta lafiya

Image caption Obama ya yi kira ga Iran ta samawa kanta lafiya

Kwanaki biyu kafin wata ziyara da aka shirya zai kai yankin gabas ta tsakiya Shugaba Obama ya yi kira ga kasar Iran ta dauki matakan gaggawa masu ma'ana na sasantawa a kan shirin nan na ta da ake cece-kuce kansa na nukiliya.

A wani sakon video na zuwan sabuwar shekara ta Iraniyawa wato Nowrouz, Shugaba Obama ya ce idan har kasar ta Iran ta dauki irin wadannan matakai, 'yan kasar za su fara ganin alfanunsa ta fuskar kyautatuwar huddar kasuwanci da sauran kasashe da suka hada da Amurka.

A ranar Laraba a karon farko a matsayinsa na Shugaban kasa Shugaban na Amurka zai ziyarci Isra'ila da mai yiwuwa kuma batun Iran ne zai zamo kan gaba a batutuwan da za su yi magana a kai.

Karin bayani