Obama ya fara ziyara a Isra'ila

Image caption Wannan ce ziyara ta farko da shugaba Obama ya kai Isra'ila tun bayan hawansa mulki

Shugaba Obama ya kara jaddada abinda ya kira dangataka ta kut-kut da babu wanda zai iya rabawa, tsakanin Amurka da Israila, bayan da ya isa Tel Aviv a ziyararsa ta farko tun darewa kan karagar mulki shekaru hudu da suka wuce.

Mista Obama ya ce Amurka na alfahari, ta goyi bayan Isra'ila a matsayinta na babbar kawa.

Shugaba Obama ya ce, "a yayinda na soma wa'adin mulki a karo na biyu a matsayin shugaba, Israila ce kasa ta farko da na ziyarata a kasar waje, kuma akwai dalili hakan."

Shugaban Isra'ila Shimon Peres da Pirayim Minista Benjamin Netanyahu ne suka tarbe shi.

Ana sa ran ziyarar Obama ta kwanaki uku za ta maida hankali a kan batun shirin nukiliya na kasar Iran, da yakin da ake yi a Syria da kuma tashin hankali tsakanin Israi'ila da Palasdinawa.

Masu sukar Shugaba Obama dai na cewa, baya da kusanci da Isra'ila, kasar da Amurkawa da dama ke ganin a matsayin babban aminiyar Amurka.

Gwamnatin fadar White House dai ta sha nanata cewa Amurka da Israila kamar Danjuma ne da Danjumai.