An rantsar da Paparoma Francis

Paparoma Francis
Image caption Dubban jama'a ne suka halarci bikin rantsar da Paparoman

Paparoma Francis ya yi bukin addu'o'i na nadinsa a hukumance a dandalin St Peters, na fadar Vatican gaban dubban mabiya darikar Katolika.

A hudubar da ya yi, sabon Paparoman, ya yi kira ga masu rike da mukamai su kare al'umma da kuma muhalli, sannan ya jaddada bukatar taimakawa talakawa.

Wakilin BBC a birnin Rome, ya ce sabon Paparoman na son ya farfado tare da yin garanbawul a fadar Vatican ta yadda za a koma amfani da koyarwar Kiristanci na asali.

Kafin a soma addu'o'in, Paparoma Francis ya karbi gaisuwa daga dubban mutane wadanda suke daga tutoci a yayin da ya leko ta saman wata mota mara rufi.

Shugabannin kasashe da na addinai daga kasashe daban-daban ne ke halartar bikin.

Karin bayani