An gano gawarwakin mutane tara a Cross Rivers

Image caption Taswirar Najeriya

Rahotanni daga jihar Cross River da ke kudu maso kudancin Najeriya, na cewa an gano gawarwakin mutane tara da daga cikin 128 da jirgin ruwa ya nutse da su.

Haka zalika an samu ceto mutane biyu da ransu daga cikin ruwan da ke da nisan mil 40 daga gabar tekun jihar Cross River.

Jami'an agaji dai sun ce suna ci gaba da neman ragowar mutanen da hadarin ya rutsa da su.

Akwai dai rahotannin da ke cewa jirgin ya taso ne daga Cross Rivers a ranar Lahadi inda ya nufi kasar Gabon da ke yankin Afrika ta Tsakiya.

Ba kasafai a kan samu hatsarin jirgin ruwa ba a Najeriya amma dai matsalar ta yi kamari a wasu kasashen Afrika, inda a harma a shekara ta 2010 wajen mutane 138 suka rasa rayukansu a lokacin da wani jirgin makure da fasinjoji ya kife a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

A shekarar dubu da takwas ma mutane 35 ne suka rasa rayukansu a lokacin da wani jirgin ruwansu ya nutse a gabar tekun Kamaru a kan hanyarsu zuwa gabon daga Najeriya.