'Mutane biliyan daya ne ke ziyartar You Tube'

You Tube
Image caption Google na samun kudaden shiga sosai da You Tube

Shafin musayar bidiyo na You Tube ya sanar da cewa a yanzu kimanin mutane biliyan daya ne ke ziyartarsa a kowanne wata.

Shafin wanda mallakar kamfanin Google ne ya ce karuwar amfani da wayoyin salula masu komai da ruwanka sun taimaka wurin karuwar jama'ar da ke ziyartar shafin a kowanne wata.

You Tube na taimakawa Google wurin samun kudaden shiga da jan hankalin kamfanonin da ke bayar da tallace-tallace, hadi da ainahin shafinsa na matambayi ba ya bata.

A shekara ta 2005 ne aka bude You Tube sannan Google ya saye shi a shekara ta 2006.

Sama da dala biliyan daya da rabi Google ya biya wurin sayen You Tube, wanda a lokacin jama'a miliyan 30 zuwa 40 ne ke amfani da shi.

Karin bayani