An sami rikici tsakanin Fulani da 'yan Atakar

Image caption Jami'an Yansandan Najeriya sun ce komai ya lafa yanzu

Rahotanni daga kudancin Jahar Kaduna sunce an samu asarar rayuka da kone konen gidaje sakamakon wani rikici tsakanin Fulani da mutanen Atakar a yau din nan.

Rikicin dai ya faru ne a masarautar Takat da Marwa dake karamar hukumar Kaura, wanda kuma ya bazu zuwa masarautar Gana-wuri da ke cikin jahar Pilato.

Yanzu haka kuma ana samun bayanai masu saba wa juna game da halin da ake ciki game da rikicin, inda wasu mazauna yankunan ke cewa har yanzu ana ci gaba da tafka rikicin,su kuwa hukumomi na cewa an shawo kan lamarin

Wani mutum wanda rikicin ya rutsa da shi ya fadawa BBC cewa an sami asarar rayuka a tashin hankalin.

A Jahar Filato ma....

Rahotanni daga karamar hukumar Wase ta Jihar Filato a Nijeriya na cewa ana ci gaba da zaman dar-dar bayan wani sabon tashin hankali da ya kunno kai daga jiya zuwa asubahin yau, lokacin da wasu mutane su ka kai hari a kauyen Mavo.

Mutane akalla goma ne dai aka bada labarin sun rasa rayukansu, kodayake dai ana samun bayanai masu cin karo da juna kan lamarin.

Karin bayani