Jonathan na neman gyara ga kasafin kudin 2013

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan ya mayar da kasafin kudin shekarar nan ta 2013 ga majalisar dokoki ta Tarayya yana neman gyara da kuma janye wasu sharudda da /yan majalisar suka saka a cikin kasafin kudin.

Shugaban ya ce irin wannan tanade-tanade ba kawai suna yin illa ga tafarkin rarrabe ikon bangarorin Gwamnati ba, a'a har ma za su iya yin tarnaki ga aikin bangaren zartaswa.

Haka kuma ya nuna rashin jin dadi game da kin baiwa hukumar sa ido a kan tafiyar da kasuwar hannayen jari ko sisin kwabo a cikin kasafin kudin.

Daga cikin abubuwan da shugaba Jonathan yake so a sauya harda batun hana kudi ga Hukumar Kula da kasuwar hannayern jari ta kasar (SEC).

'Yan majalisar dai sun hana hukumar ko kwabo suna masu cewa sai gwamnati ta kori shugabar hukumar Aruma Oteh.

Ya kuma nemi su rage kudaden da suka sanya na gudanar da ayyukan raya kasa a mazabunsu.

Har ila yau shugaban ya nemi 'yan Majalisar su janye sharudan da suka kafa na sa dio kan yadda za a aiwatar da kasafin kudin duk bayan watanni uku, yana mai cewa hakan, zai yi illa ga ikon da bangaren zartaswa ke da shi.