Mutane 29 ne suka tsira a hadarin Cross River

Image caption Taswirar Najeriya

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da cewa mutane 29 ne suka tsira da rayukansu bayan da wani karamin jirgin ruwa ya kife a kusa da gabar tekun Cross River da ke kudu maso kudancin kasar ranar Juma'a.

Cikin wadanda suka tsiran har da mutane biyu wadanda suka sha ta hanyar makalewa a jikin wata tukunyar iskar gas na girki--

A wata sanarwa da ya aikewa BBC, kakakin Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriyar, NEMA, Malam Yusha'u Shu'aibu, ya bayyana cewa jirgin na dauke ne da fasinjoji 128, kuma an samu gawarwakin tara daga cikinsu.

Jirgin dai ya taso ne daga Jamhuriyar Benin mai makwabtaka da Najeriyar zai je Gabon, amma ya yada zango a garin Oron da ke jihar ta Cross River.

Sa'o'i biyu bayan nan ne kuma matsalar inji ta kai ga nutsewar jirgin.

Ba kasafai a kan samu hatsarin jirgin ruwa ba a Najeriya amma dai matsalar ta yi kamari a wasu kasashen Afrika, inda a harma a shekara ta 2010 wajen mutane 138 suka rasa rayukansu a lokacin da wani jirgin makure da fasinjoji ya kife a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

A shekarar dubu da takwas ma mutane 35 ne suka rasa rayukansu a lokacin da wani jirgin ruwansu ya nutse a gabar tekun Kamaru a kan hanyarsu zuwa gabon daga Najeriya.

Karin bayani