Gwamnati Cyprus za ta bullo da sabon shirin

Image caption Bankuna a Cyprus za su ci gaba da zama a kulle har sai ranar Talata

Shugaban kasar Nicos Anastasiades zai gabatar da wani shirin na dabam na taimakawa kasar wajen samun tallafi daga manyan kasashen duniya a kokarin da kasar ke yi na gujewa durkushewar tattalin arzikin.

Ba'a dai bayyana matakin da kasar za ta dauka ba, amma dai akwai majiyoyin da ke cewa Kasar Rasha za ta taimakawa a wannan sabon shirin.

Har yanzu dai ana jiran tsammani ne a kasar ta Cyprus domin neman mafita daga matsalar tattalin arziki da ya addabi kasar a kusan shekaru arba'in kenan.

Kasar dai sannu a hankali na kan hanyar durkushewa ne.

A yau ne dai kuma ake ganin shugabanin siyasar kasar za su tattauna kan lallubo hanyoyin da za su taimaka wajen taimakawa tattalin arzikin kasar.

Wasu daga cikin hanyoyin da ake ganin yan siyasar za su nema shine, baiwa gwamnatin kasar ikon mallakar kudaden ajiya na fansho da kuma sanyawa Bankuna haraji madaidaici ba kamar yadda aka yi kokarin a yi a baya ba.

Har wa yau Bankunan kasar za su ci gaba da zama a kulle har zai ranar Talata mai zuwa, domin kada masu ajiye su kwashe kudaden su.

Ministan kudin Cyprus dai a yau dinan zai tattauna ne da takwaransa na kasar Rasha a kokarin da kasar ke yi na neman taimako daga kangin da ta ke ciki.