A bayyyana masu kai hari! Inji Sarkin Kano

A Nigeria, mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, ya yi kira ga gwamnati da ta mayar da hankalin nemo mutanen da ke shirya tashe tashen hankulan da ke addabar kasar, musamman ma arewacin kasar.

Ya ce ya kamata a bayyana su kowa ya san su.

Sarkin na magana ne a lokacin da ya karbi wata tawagar gwamnatin tarayya da ta kai masa ziyarar jaje a fadarsa.

Kiraye kirayen neman hanyoyin samar da zaman lafiya a Najeriyar dai sun karu ne tun bayan harin da aka kai a yankin Sabon Gari dake a Kanon wanda ya janyo mutuwar mutane fiye da 20 a farkon wannan makon.

A wani labarin kuma kungiyar Jama'atul Nasrul Islam a Najeriya ta yi Allah -wa-dai da harin Bom din da aka kai a wata tashar manyan motocin haya a unguwar Sabon Gari dake Kano.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Kaduna kungiyar ta ce harin Bom din ba wani abu ba ne illa kokarin wasu na haddasa fitina a kasar baki daya, musamma don kara baraka tsakanin Musulmi da kuma kirista.