Za'a binciki Nicolas Sarkozy

Image caption Tsohon shugaban Faransa na musanta zargin da ake masa

Za fara binciken tsohon shugaban kasar Faransa Nicols Sarkozy saboda ana zarginsa da karbar wasu kudade daga wajen wata hamshakiyar attajira Lilian Bettencourt.

Wani alkalin kotu dai ya bukaci Mista Sarkozy ya bayyana a gabanta a Bordeaux inda ya amsa zargi da wani ma'ikacin attajiran ya yi masa na cewa ya karbin kudin kamfe daga wurinta domin tafiyar da yakin neman zabensa a shekara ta 2007.

Mitsa Nicolas Sarkozy ya yi magajin garin wani yanki mai dumbin arziki a birnin Pari. A nan ne kuma ya san matar da ta fi kudi a kasar Faransa.

Bayan wasu shekaru Mista Sarkozy ya kusanci Lilliane Bettencout sosai. Wani ma'aikacinta ya ce a koda yaushe Mista Sarkozy yana ziyartar gidanta.

Amma zargin da ake masa yanzu shine gabanin zaben shekarar 2007, Mista Sarkozy yayi amfani da kusancinsa da ita da kuma shekarunta wanda a yanzu haka take shekaru casa'in da ya haihuwa, inda ya karbi wasu makudan kudade domin tafiyar da yankin neman zabensa.

Wani ma'aikacin Miss Bettencourt ya ce shi da kansa ya mikawa manajan Kamfe din Mista Sarkozy, Eric Woerth dubban kudin euro kuma a wasu lokutan Mista Sarkozy ne ya zo da kansa ya karbi kudin.

Mista Sarkozy wanda ke nuna kwadayin sake tsayawa takara a shekara ta 2017 ya nace cewa sau daya ne ya taba ziyartar gidan Miss Bettencourt a shekara ta 2007.

A jiya ya amsa tambayoyi daga wani alkali kan alakar tasa da attajiran inda bayanan da ya bayar ya ci karo da na ma'aikacinta wanda shima ya bayyana a gaban kotun.

Bayan Mista Sarkozy ya gama amsa tambayoyin ne kotun ta ce za'a bincike shi game da batun.

Binciken da za'a gudanar ne zai tabbatar da cewa ko za'a gurfanar da Mista Sarkozy a gaban kotu ko a'a.

Karin bayani