Hare-hare a garin Ganye da ke Adamawa

Image caption Yankin arewa masu gabashin Najeriya na fama da hare-hare

Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya na cewa an kai wani hari a garin Ganye da ke kudancin Jihar Adamawa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Muhammad Ibrahim, ya tabbatar da faruwar al'amarin da maraicen jiya Juma'a.

Mazauna garin dai sun ce sun ji karar harbe-harbe da fashewar abubuwa a wajen gidan yari da ofishin 'yan sanda da sakatariyar karamar hukumar Ganye.

Ya zuwa yanzu dai ba'a tabbatar da yawan mutane da suka jikkata ko rasa rayukansu ba.

Amma wadanda suka gane wa idonsu sun shaidawa BBC cewa an samu asarar rayuka.

Tuni dai Hukumar yansanda ta ce ta kara tsaurara tsaro a garin da kewa a yayinda al'ummar gari ke cikin fargaba.

Ya zuwa yanzu dai ba'a san wadanda suka kaddamarda harin ba, kuma babu kungiyar da ta yi ikirarin cewa ita ta kaddamar da harin.