Jama'a na ficewa daga Bangui

Praministan janhuriyar Afurka ta tsakiya, Nicolas Tiangaye, ya yi kiran tattaunawa tare da 'yan tawaye wadanda ke nausawa zuwa babban birnin kasar, domin kaucewa tashin hankalin da zai kai ga zubda jini.

Wannan kiran dai ya zo yayin da 'yan tawayen Seleka ke dab da shiga birnin Bangui, biyowa bayan rushewar yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma watanni biyun da suka wuce.

Kungiyar 'yan tawayen ta Seleka dai ta ce a shirye ta ke ta tattauna da shugabannin Afurka domin warware rikicin, wanda ya jawo damuwa ga kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya, amma ta yi watsi da duk wani kiran tattaunawa da shugaba Fransuwa Bozize.

Daya daga cikin manyan kwamandojin sojin kungiyar 'yan tawayen ya ce baza su shiga wata tattaunawa da gwamnatinsu ba domin sun sha yin hakan ba tare da an ga wani canji ba.

Ya kuma kara da cewa muddin su ka samu kaiwa cikin birnin Bangui to kuwa za su kafa sabuwar gwamnati ne.

Ranar 10 ga watan Desemba ne dai hadakar kungiyoyin 'yan tawayen 3 da suka dunkule suka kafa Seleka suka fara kai harinsu na farko a arewacin kasar, inda suke zargin shugaba Bozize da kin mutunta yarjeniyoyin da suka kulla tun da farko.

Yanzu haka mazauna birnin Banguin sun ce suna cikin fargaba yayin da tuni wasu suka fara ficewa daga birnin.