An fara bincike kan rasuwar Berozovsky

Boris Berozovsky
Image caption Boris Berozovsky yana fama da dinbin bashi

Masana kan sidarai masu guba a Burtaniya na gudanar da bincike kan mutuwar wani hamshakin dan kasuwa na kasar Rasha Boris Berezovsky - wanda ya rasu a gidansa da ke kusa da birnin London.

A baya Mr Berezovsky, yana da alaka da gwamnatin Rasha, sannan ya mallaki dukiya sosai lokacin da tarayyar Soviet ta wargaje.

Sai dai daga baya ya raba-gari da shugaba Putin, inda ya rinka sukar shugaban, sannan ya yi gudun hijira zuwa Burtaniya.

Mai magana da yawun shugaba Putin Dmitry Peskov, ya ce Berezovsky ya so komawa gida:

"A 'yan watannin da suka gabata, Mr Berezovsky ya aike da wasika wacce ya rubuta da hannunsa ga shugaba Putin - yana bayyana kuskurensa tare da neman afuwa da kuma izinin ko zai samu damar komawa kasarsa ta haihuwa".

A 'yan kwanakin nan Mr Berezovsky na fuskantar matsi a harkokinsa na kasuwanci bayan da ya sha kayi a wata shari'a ta biliyoyin daloli a hannun takwaransa na Rasha Roman Abramovich.

Wakilin BBC yace marigayi Berozovsky yana cikin hamshakan attajirai 'yan kalilan da suka yi arziki bayan rushewar tsarin kwaminisanci.

Marigayin ya yi arziki ne yayin sayar da kamfanoni mallakar gwamnatin Rasha ga 'yan kasuwa cikin shekarun 1990, amma kuma daga baya ya tsunduma cikin dabaibayin bashi.

Karin bayani