An fatattaki masu kishin Islama daga Gao

A garin Gao dake arewacin Mali, sabon fada ya barke tsakanin 'yan tawaye masu kaifin kishin Islama da kuma dakarun kasar.

Wata majiyar sojan Malin tace, yayin fadan an kashe mutane bakwai, da suka hada da masu kaifin kishin Islama hudu, da fararen hula biyu da kuma sojan Mali guda.

Mai magana da yawun sojojin Mali, Sulaiman Maiga ya ce an fatattakin 'yan tawayen da misalin karfe goma na daran jiya bayan kwashe sa'o'i 2 ana bata kashi.

Kakakin sojin ya ce 'yan tawayen sun silalo cikin garin Gawo ne ta wuraran binciken motoci na soji kuma har suka kai tsakiyar birnin.

Anan ne suka bude wuta da gurneti a wajan dakarun Nijar ke tserewa.

Har ila yau kuma sun kai hari kan dakarun sojin Mali gabanin a fara bata kashi a wani yanki da jama'a suke.

An kwatanta farar hular da aka kashe da cewa wani matashi ne dake kan babur.

Kakakin sojin ya ce bai san maharan ko 'yan wace kungiya ba ne amma wadanda aka kashen yan kasashen waje ne.

Dakarun sojin Faransa sun samu sake kwace garin Gao ne dake da nisan kilo mita 250 ta gabashin Timbuktu daga hannun 'yan tawayen makwanni biyi da zuwansu Mali a watan Janairu.

Yanzu haka dakaru soji dubu 4 ne ke maida hankali a yankin Ifaghas dake da tsaunuka wanda ke kusa da kasar Algeria.

Fadan da akai ranar asabar da daddare dai ya biyo bayan wani harin bam da aka kai da mota ranar alhamis a kusa da filin saukar jiragen sama na Timbuktu.

Wadannan hare hare 2 da akai kai sun sake sa fargaba a zukatan mutane ganin cewa yanzu da dakarun Faransa suka sauya alkiblarsu, yan tayen su dawo da kai hare hare a gururuwa kamar su Gao.