Shirye-shiryen zabe a Pakistan

Tsohon shugaban Pakistan, Pervez Muhsarrafa ya koma gida bayan ya shafe shekaru hudu yana gudun hijira.

Jirgin da ya dauko shi ya sauka a birnin Karachi inda daruruwan magoya bayansa suka yi masa gagarumar tarba.

Janar Musharraf dai yana shirin jagorantar jam'iyyarsa ne a zaben kasa baki daya da za'a yi cikin watan Mayu.

Musharraf ya kuma fadawa BBC cewa, ya ji dadin komawa gida Pakistan, amma yace, yana sane da irin hatsarin da zai fuskanta.

Kungiyar Taliban dai tayi barazanar cewa, zata kashe shi, kuma tuni Musharraf din ya soke wani gangami da ya shirya yi.