Pervez Musharraf ya koma Pakistan

Pervez Musharraf
Image caption Musharraf ya wallafa hotonsa a cikin jirgi a shafinsa na Twitter

Jirgin da ke dauke da tsohon shugaban kasar Pakistan Pervez Musharraf, ya sauka a birnin Karachi na kasar duk da barazanar da Taliban ta yi na kashe shi.

Ya nanata cewa ba ya tsoron barazanar da kungiyar Taliban ta yi na kashe shi ta hanyar amfani da 'yan kunar bakin wake.

Janar Musharraf ya ce kungiyar ta Taliban ta yi kokarin hallaka shi a baya ba tare da nasara ba, amma zai yi kokarin kare kansa.

Yana kokarin jagorantar jam'iyyarsa ne a zaben kasar ta Pakistan da za a yi a watan Mayu.

Harin kunar bakin wake

A ranar Juma'a ne mahukuntan Pakistan suka bashi beli tare da kariya kan tuhume-tuhumen da ake masa - wanda zai sa ya iya shiga kasar ba tare da an kama shi ba nan take.

Wani sako da ya aika a shafin Twitter, ya ce "na zauna tsaf a kujerar jirgi domin komawa gida Pakistan".

A kan hanyarsa ta tafiya filin saukar jiragen saman, Janar Musharraf cikin fara'a, ya gaya wa wakiliyar BBC Orla Guerin cewa, ji yake kamar zai tafi bikin aure.

A gefe guda kuma, wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam a wani wurin binciken ababan hawa a yankin Arewacin Waziristan na kasar ta Pakistan, inda ya kashe sojoji goma sha bakwai.

Harin ya faru ne a tsakiyar daren ranar Asabar.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin lamarin.

Arewacin Waziristan yana kusa da iyakar kasar ne da Afghanistan, kuma wuri ne da ake ma kallon cibiyar kungiyar Taliban da kuma Al-Qaeda.

Karin bayani