An yanke wa Okah daurin shekaru 24

 Henry Okah
Image caption Henry Okah ya yi niyyar daukaka kara kan hukuncin

Wata kotu a kasar Afrika ta Kudu ta yankewa dan Najeriya Henry Okah hukuncin daurin shekaru 24 a gidan yari kan tagwayen hare-haren bama-baman da aka kai a Abuja a 2010.

"Mutumin da ake zargi Okah, an yanke masa hukuncin zaman gidan kaso na shekaru 24," a cewar alkalin kotun Neels Claassen.

Mutane 12 ne aka kashe a harin bam din wanda aka kai a ranar bikin cikar Najeriya shekaru 50 da samun 'yan cin kai.

Kungiyar 'yan gwagwarmaya ta yankin Niger Delta Mend - wacce Okah ke jagoranta, ta ce ita ce ke da alhakin harin.

Tashe-tashen hankula sun ragu

Babu tabbas ko Najeriya za ta nemi a mika mata shi domin ya yi zaman gidan kason a kasar ko kuma a'a.

Masu gabatar da kara sun ce duk da cewa Okar ba dan kasar Afrika ta Kudu ba ne, kasar na da ikon yin masa shari'a karkashin dokar kasa-da-kasa ta International Co-operation in Criminal Matters Act.

An kama Okah ne kan zargin mallakar makamai a kasar Angola a shekara ta 2007 sannan aka mika shi zuwa Najeriya sai dai ba a same shi da laifi ba.

An sallame shi bayan shekaru biyu karkashin afuwar da aka yi wa masu tayar da kayar baya sannan ya koma Afrika ta Kudu inda ya ke da zama tun shekara ta 2003.

Tashe-tashen hankula sun ragu matuka bayan da gwamnati ta yi wa 'yan gwagwarmayar afuwa a shekara ta 2009.

Karin bayani