Birtaniya za ta tsaurara ka'idoji a kan baki

cameron
Image caption Pirayi Ministan Birtaniya, David Cameron

Pirayi Ministan Birtaniya, David Cameron ya sanar da shirinsa na tsaurara ka'idoji na yawan kudaden da za a iya biyan baki a cikin kasar.

'Yan cirani daga kasashen da suka fito daga cikin tarayyar Turai, za suyi hasarar kudaden da ake basu na rashin aikin yi bayan watanni shida, har sai in sun iya samar da wata hujja gamsashiyya dake nuna cewa sun kasa samun aikin yi.

Za kuma a tsaurara ka'idojin da aka sanya a kan aikin yin da ba halartacce ba.

Mista Cameron ya ce yawan 'yan cirani dake shigowa cikin kasar ya yi yawa sosai, amma gwamnati tana maraba da 'yan cirani dake aiki tukuru.

Akwai damuwa game da sabbin 'yan ciranin da za su shigo Birtaniya idan har aka dage takaita zirga zirgar mutane daga kasashen Bulgaria da Romania daga farkon shekara mai zuwa.

Karin bayani