Fursunoni sama da 120 ne suka tsere a Najeriya

Image caption Ana samin yawaitar kubutar da fursunoni a Najeriya

Fursunoni sama da dari daya da ashirin ne aka ba da rahoton sun tsere a gabashin Najeriya bayan wasu mutane dauke da makamai sun balle kofar gidan Yari da dakunan da ake tsare da su da karfin tsiya.

Shugaban gidan Yarin Andrew Barka, ya ce fursuna daya kadai aka bari bayan an harbe shi an yi masa rauni.

Gidan Yarin ya na daya daga cikin wuraren da aka kai wa harin a garin Ganye dake kan iyaka da kasar Kamaru.

An kuma kaiwa wani banki harin da wani gidan barasa guda.

Kungiyar nan ta Boko Haram ce ake zargi da kai hare-haren nan daya-bayan-daya wanda 'yan sanda suka ce an kashe mutane ashirin da biyar.

A yammacin ranar Jumma'a ne aka kai hare-haren, amma sai yanzu ne bayanan ke dada fitowa.

Karin bayani