Abu Qatada ya yi nasara a kotu

Abu Qatada
Image caption Ma'aikatar cikin gida ta Burtaniya ta ce za ta daukaka kara

Sakatariyar harkokin cikin gida ta Burtaniya Theresa May, ta sha kayi a shari'ar da ta shigar tana neman tasa kyayar wani malamin addini Abu Qatada zuwa kasar Jordan.

A bara, hukumar daukaka kara kan shige da fice ta musamman ta ce ba zai yi wu a mika malamin addinin musuluncin ga Jordan ba.

Alkalan sun ce ba za a yi masa adalci a ba - za a iya amfani da shaidun da aka samu ta hanyar muzgunawa wasu.

Ma'aikatar cikin gida ta Burtaniya ta ce za ta daukaka kara.

Ta kara da cewa: "Wannan ba shi ne karshen zancen ba. Gwamnati a shirye ta ke ta tasa kyayar Abu Qatada."

Mai magana da yawun ma'aikatar ya ce a yanzu, "Za mu ci gaba da aiki tare da kasar Jordan domin shawo kan batutuwan shari'ar da ke kawo tsaiko ga batun".

Hukuncin kotun daukaka karar na nufin za a saki Abu Qatada makonni biyu bayan kama shi.

Karin bayani