'Yan adawar Syria sun nemi taimakon makamai

arab
Image caption Jagoran 'yan adawa a Syria, Moaz al-Khatib

'Yan adawar kasar Syria, a karon farko sun dare kujerar wakilcin Syriar a taron kolin Kungiyar Kasashen Larabawa.

Sarkin Qatar, wanda ke jagoratar taron kolin, shi ne a hukumce ya gayyaci 'yan adawar cewa su maye gurbin gwamnatin Syriar a kan wannan kujera.

Mahalarta taron sun yi ta sowa da tafi a lokacin da tawagar 'yan adawar ta mutum-hutu suka zauna a kan kujerunsu, karkashin jagorancin Mo'az Al Khatib, wanda a 'yan kwanakin nan ya mika takardar murabus dinsa a matsayin jagoran 'yan adawar, amma aka rarrashe don ya ci gaba.

Daya daga cikin jagoran 'yan adawar Syria a lokacin taron ya nemi Amurka ta taimaka wajen kare yankunan da 'yan tawaye suka kama a Syrian ta hanyar amfani da makamai masu kakkabo makamai masu linzami.

Sai dai kungiyar tsaro ta NATO ta maida martani ba tare da wani bata lokaci ba, tana mai watsi da wannan roko.

Karin bayani