Taron Kasashe masu tasowa na BRICs

BRICs
Image caption Kasashen na kuma son bunkasa kasuwanci da nahiyar Afrika

Kasashe masu tasowa da ke gaba-gaba a bunkasar tattalin arziki (BRICs) na taro a birnin Durban na Afrika ta Kudu, inda ake sa ran za su assasa shirye-shiryen bullo da wata hukuma da za ta zama kishiya ga hukumomin IMF da Bankin duniya.

Shugabannin Brazil, da Rasha, da India, da kasar Sin da kuma Afrika ta Kudun, da a takaice ake kira BRICs, za su kuma maida hankali a kan yadda za a inganta ci gaban tattalin arziki, wanda ya dan soma jan kafa a cikin dukkan kasashen na su.

Jagoran da ke kula da fannin tsimi da tattali na kamfanin na Goldman Sachs, Jim O'Neil, shi ne ya fito da wannan sunan na BRICs a shekara ta 2011.

Wadannan kasashe dai a tsakaninsu, suna da kashi 43 cikin dari na yawan al'ummar duniya.

Karfin tattalin arziki

Sannan kuma sune ke da kashi 17 cikin dari na harkokin kasuwancin da ake yi a fadin duniya baki daya.

Bugu da kari, su ke samar da kashi daya bisa hudu na dukiyar da ake samu a duniya.

Wani rahoto na baya-bayan nan da ya fito daga Majalisar Dinkin Duniya, ya nuna cewa nan da shekara ta 2020, karfin tattalin arzikin uku daga cikin kasashen kungiyar - Brazil da China da India kadai, zai zarta abun da kasashen Canada da Faransa da Italiya da Brittania da kuma Amurka ke kerawa.

Masu sha'awar kungiyar ta BRICs dai za su shafe wannan makon suna nuni ga irin matsalolin da kasashen kungiyar Tarayyar Turai ke fuskanta da kuma rikicin tattalin arzikin da ake fama da shi a Cyprus.

Abin da kuma zai kara bayar da karfin guiwa ga tawilin da ake yi cewar ginshikan harkokin tattalin arziki ta duniya na sauyawa, kuma kasashen BRICs na tsakiyar wannan sauyi.

Daya daga cikin mahimman abubuwan da za a tattauna a wannan taro na Durban, shi ne yiwuwar assasa shirin bullo da wani banki na kasashen kungiar ta BRICs.

Akwai matukar bukata ta kirkiro da bankin rayan kasashen, wanda manufarsa shi ne tabbatar da samar da manya- manyan abubuwan da tattalin arziki ke dogara akansu a kasashen kungiyar.

Daya daga cikin abin da ya haifar da wannan abu kuwa shi ne, yadda wasu daga cikin 'yan kungiyar suke dari-dari da hukumomi kamar na bada lamuni ta duniya da kuma babban bankin duniya.

Wannan dai shi ne taro na biyar na kungiyar ta BRICs, amma kuma na farko a nahiyar Afrika.

Wani abu guda da zai ja hankali shi ne yawan kasuwancin da wadannan kasashe ke yi da nahiyar baki daya.

Ko da ya ke kuma kamar yadda Shugaban China Xi Jinping ya bayyana a Tanzania, suna yiwa nahiyar kallon abokiyar kawance ba wadda za'a ci da guminta ba.

Karin bayani