Za a ci gaba da rufe Bankuna a Cyprus

Image caption Za a ci gaba da rufe Bankuna a Cyprus zuwa Alhamis

Bankuna a kasar Cyprus za su cigaba da kasancewa a rufe har zuwa ranar Alhamis sannan kuma za a gitta wasu sharudda na hurdodin kudi zuwa wani dan lokaci bayan an sake bude su duk kuwa da bashin da aka samu daga hukumomi masu ba da lamuni.

Babban bankin Cyprus ya ce, rufe bankunan zuwa wani lokaci mai tsawo zai tabbatar da gudanar harkokin bankunan cikin tsanaki.

Tun farko Shugaban kasar ta Cyprus Nicos Anasta-siades ya kare bashin da aka karba.

Mr Anasta-siades din wanda ya kulla yarjejeniyar da Babban bankin Tarayyar Turai da asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ya ce yarjejeniyar tana da ciwo, to amma ita ce hanyar kawai da ta rage a bi.

Yarjejeniyar ta bayar da kariya ga kananan masu ajiya, amma masu kudi da suka haura euro dubu dari a bankuna wadanda akasarinsu 'yan Rasha ne suna fuskantar hasara mai dimbin yawa.

Karin bayani