'An kama mota makare da makamai a Kano'

Kwamishinan 'yan sanda na Kano Musa Daura
Image caption Jihar Kano ta dade tana fama da hare-haren 'yan bindiga

'Yan sanda a jihar Kano ta Nigeria sun ce sun kama wata mota kirar Golf makare da makamai a kauyen Inusawa da ke karamar Hukumar Ungogo.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Musa Daura, ya shaida wa 'yan jarida a Kano cewa, an kama motar ne mai lamba AG 701 KTN, ranar Talata da misalin karfe 9.30 na dare bayan da suka samu bayanan sirri.

"Lokacin da mutanen da ke cikin motar suka hango jami'an sunturi sai suka bude wuta amma nan take sai mutanenmu suka mayar da martani.

"Wannan ne ya sa masu motar suka fice suka shige daji da raunukan bindiga a jikinsu," a cewarsa.

Kwamishinan ya ce bayan da suka binciki motar sai suka gano makamai da suka hada da bindiga samfurin AK-47, da kuma alburusai 238.

Sauran abubuwan sun hada da alburusan Ak-47 guda takwas, da gwangwanin mai na Turkey bakwai mai dauke da bam da tukwanen gas guda biyu.

Jihar ta Kano na daya daga cikin jihohin arewacin kasar da ke fama da hare-haren 'yan bindiga, na baya-bayan nan shi ne wanda ya kashe mutane fiye da 20 a tashar motoci ta Sabon Gari.

Karin bayani