Ntaganda ya gurfana a gaban kotun ICC

Bosco Ntaganda
Image caption Ntaganda ya yi yaki tare da kungiyoyin 'yan tawaye daban-daban da kuma rundunar sojin kasar ta Congo

Mutumin da ake zargi da aikata laifukan yaki a Congo Bosco Ntaganda ya bayyana a gaban kotun hukunta laifukan yaki ta duniya ICC, a karon farko tun bayan da ya mika kansa.

Mr Ntaganda wanda ya taka rawa a rikicin da ake yi a Gabashin Congo ya musanta aikata laifukan yaki da na cin zarafin bil'adama.

Ya shaida wa kotun cewa bai amince da lafin da ake tuhumarsa da aikata wa, kafin alkali ya katse masa hanzari da cewa ba za a bukace shi yace wani abu a kan tuhumar da ake masa ba, har sai a zaman shari'a na gaba.

Yana fuskantar tuhume-tuhume 10, da suka hada da fyade, da kisan kai da kuma tilastawa yara shiga aikin soji.

Janar Ntaganda ya mika kansa ga ofishin Jakadancin Amurka a Rwanda, a ranar 17 ga watan Maris, sannan aka mika shi zuwa birnin Hague inda kotun ta ke.

Ya yi yaki tare da kungiyoyin 'yan tawaye daban-daban da kuma rundunar sojin kasar ta Congo.

Na baya-bayan nan, shi ne amannar da aka yi cewa yana daya daga cikin kwamandojin kungiyar 'yan tawaye ta M23 wacce ke yakar dakarun gwamnati a Kudancin kasar.

A kotun, an shaida wa Janar Ntaganda laifukan da ake tuhumarsa da aikata wa sannan aka gaya masa cewa za a zauna shari'a a ranar 23 ga watan Satumba domin duba yiwuwar ko akwai cikakkun hujjoji domin ci gaba da shari'ar.

Ya shaida wa kotun cewa shi haifaffen kasar Rwanda ne amma ya taso ne a Congo kuma dan kasar ta Congo ne.