Za a bude Bankunan Cyprus ranar Alhamis

Image caption Za a bude bankuna a Cyprus

Gwamnan babban bankin Kasar Cyprus Panicos Demitriades ya yi alkawarin abinda ya kira namijin kokari na sake bude bankunan Kasar a ranar Alhamis.

Bankunan dai sun shafe kusan makonni biyu a rufe domin hana mutane kwashe kudadensu na ajiya, a yayinda ake tattaunawa akan shirin ceto tsarin bankunan Kasar daga durkushewa.

Gwamnan Demitriades ya yi kalaman ne lokacinda yake amsa tambayoyi a wani taron manema labarai.

Lokacinda aka tambaye shi, ko akwai hadarin da zai hana a bude bankunan; Mr Demitriades din ya ce a'a, akwai namijin kokari da aka yi na sake bude su a ranar Alhamis.

Mr Demitriades din ya tabbatar da cewa za a sanya harajin kusan kashi arba'in cikin dari akan masu ajiya a banki da kudadensu ya haura dala dubu dari da talatin, kuma ya yi gargadin za a takaita wata mu'amallar.

Karin bayani