A Somalia ana yi wa 'yan gudun hijira fyade

Image caption Ana yiwa yan gudun hijira fyade a Somalia

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human rights watch ta ce mutanen da aka tilasta wa tserewa daga gidajen su a Somalia suna fuskantar matsaloli da dama da suka hada da fyade da sauran gallazawa daga kungiyoyi masu dauke da makamai, har ma da sojojin gwamnati.

Human rights watch din ta ce matan da suka tsere wa yunwa da fadace-fadace suka koma suna zama a sansanonin 'yan gudun hijira dake Mogadishu sun bayyana irin yadda wasu Maza dake sanye da kayan soji da masu rike da makamai ke yi musu fyade.

Kungiyar ta ce masu kula da sansanonin wadanda mafi yawan lokuta suna da alaka da kungiyoyin masu dauke da makamai, su kan kuma wasashe abinci da sauran wasu kayan agaji.

Gudanar da sansanonin dai ya zamo wata hanya ta samun abin duniya, kungiyar ta ce, masu kula da sansanonin suna hana wadanda ke zaune cikinsa rayuwa.

Karin bayani