An sace 'yan Labanon 3 a Najeriya

'Yan sandan Najeriya
Image caption Garkuwa da mutane a Najeriya

Rahotanni daga Legas a Kudancin Najeriya na cewa an sace wsau 'yan Kasar Labanon su uku a unguwar victoria island.

Sace mutanen uku na zuwa ne kuma daidai lokacin da aka bada labarin cewa an saki wani dan Birtaniya wanda aka sace a birnin na Legas na Najeriya a karshen makon daya wuce.

Koda yake dai sace 'yan kasashen waje a Legas sabon abu ne, amma dai an shafe shekaru ana garkuwa da 'yan kasashen wajen a yankin Naija Delta mai arzikin mai a Najeriya a yayinda a Arewacin kasar kungiyar masu tada kayar baya na musulmi kan yi garkuwa da 'yan kasashen waje.

Karin bayani