Bankuna sun buɗe a Cyprus bayan makonni na Ƙila-wa-Ƙala

Bankin Cyprus
Image caption Bankin Cyprus

An nemi tsaffin alƙalan Kotun Ƙolin ƙasar Cyprus uku, su gudanar da bincike a kan yiwuwar aikata ba daidai ba a rikicin bankunan da kasar ke fama da shi.

Gwamnatin Cyprus ta ce alkalan za su duba dukkan matakai da ayyukan da aka gudanar ne a kowanne mataki.

Shugaban ƙasar ta , Nicos Anastasiades, ya yaba wa jama'ar ƙasar a kan abin da ya kira hankalin da suka nuna a lokacin da bankuna suka ‘ a karon farko cikin kusan makonni biyu.

An dai samu dogayen layuka a bankunan.

Wakilin BBC ya ce, “Hukumomin ƙasar ta Cyprus da na Tarayyar Turai sun ce, an taƙaita yawan kuɗin da masu ajiya a bankuna za su iya fitarwa ne har zuwa wani lokaci.

Amma dai ba wanda ke da cikakkiyar masaniya.