An ba da rahoton rasa rayukan baƙaƙen fata

Bakaken fata a Libya
Image caption Bakaken fata a Libya

Rahotanni na cewa 'yan ƙasar Nijar da dama da kuma sauran baƙaƙen fata da ke zaune a Libya ne suke rasa rayukansu sakamakon azabtarwar jami'an tsaron Libya.

Hukumar kula da ‘yan Nijar mazauna kasashen waje ta tabbatar da labarin, sai dai ta ce zuwa yanzu ba a kai ga tantance adadin wadanda suka rasu ba.

Wasu rahotannin kuma na cewa, jami'an tsaron Libyan suna ci gaba da kama baƙi baƙaƙe 'yan ƙasashen waje.

To tuni dai hukumomin jamhuriyar Nijar ɗin suka mayar da martini dangane da rahotannin da ke cewa wasu 'yan Nijar ɗin da dama sun rasa rayukan nasu sannan wasu dubbai na tsare a kasar Libiya.