Lauyoyin Pistorius za su kalubalanci beli

Lauyoyin zakaran tseren nakasassu Oscar Pistorius za su kalubalanci sharudan bada belin sa a wajen sauraron karar da za a yi a yau a Afrika ta kudu.

Ana dai zargin Mista Pistorius ne da kisan budurwarsa Reeva Steenkamp a gidansa a watan da ya gabata.

Sai dai kuma Mista Pistorius ya musanta zargin da ake masa, inda ya ce ya harbe ta ne bisa tunanin wani ne ya shigo masa gida.

Lauyoyin nasa dai za su bukaci da abar sa ya koma gidansa da kuma yin tafiye-tafiye.

An bayar da belin dan tseren Afrika ta Kudu Oscar Pistorius, wanda ake tuhuma da kisan budurwarsa, bayan wani dogon zaman jin bahasi.

Sharadn belin sun hada da ya rinka mika kansa ga jami'an 'yan sanda sau biyu a kowanne mako.

Ya biya kudin beli dala 113,000 wato miliyan daya na kudin Rand na Afrika ta Kudu, tare da wasu mutanen da su ka tsaya masa.

Sannan an kwace dukkan makaman da ya mallaka tare da hana shi shan giya.