An sassauta belin Oscar Pistorius

Dan tseren wasan nakasassu na Afrika ta Kudu Oscar Pistorius, wanda ake tuhuma da kisan budurwarsa, za a bashi damar tafiye-tifiye bayan da ya kalubalanci sharudan belinsa.

Alkalin kotun ya ce dan tseren na Olympics da Paralympic zai iya barin Afrika ta Kudu domin shiga wasanni a kasashen ketare matukar dai ya bi sharudan da aka kafa masa.

Za kuma a bashi damar koma wa gidansa a birnin Pretoria, inda aka harbe Reeva Steenkamp.

Mr Pistorius ya musanta harbe Reeva, mai shekaru 29 da gan-gan, inda ya ce ya harbe ta ne bisa tunanin wani ne ya shigo masa gida.

Tun da farko lauyoyinsa sun bukaci da abar shi ya koma gidansa da kuma yin tafiye-tafiye.

An bayar da belin dan tseren ne, wanda ake tuhuma da kisan budurwarsa, bayan wani dogon zaman jin bahasi.

Sharadn belin sun hada da ya rinka mika kansa ga jami'an 'yan sanda sau biyu a kowanne mako.

Ya biya kudin beli dala 113,000 wato miliyan daya na kudin Rand na Afrika ta Kudu, tare da wasu mutanen da su ka tsaya masa.

Sannan an kwace dukkan makaman da ya mallaka tare da hana shi shan giya.