JTF ta gano wajen tara makamai a Kano

Rundunar tsaron hadin gwiwa ta JTF da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Kano tace ta gano wajen tara makamai na masu kai hare- hare a birnin na Kano.

Rundunar tace ta samu makamai da dama gami da kama mutane biyar wadan da ake zargi suna cikin masu tsarawa da kai hare -hare a birnin na Kano.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce an samu makaman ne a unguwar Gaida ajawa bayan wani bincike da jami'an tsaro suka gudanar.

Sanarwar ta ce bindigogi dabam-dabam ne, goma sha shida har da mai jigida aka gano da kuma AK 47 guda shida da alburasai da dama da abubuwan da ake jefawa da hannu.

Har wa yau rundunar ta ce ta gano wasu ruwan sinadarai da takin zamani da ake hada abubuwan fashewa.

Rudunar tsaron tace ta kame mutane shida a wuraren dabam-dabam a cikin jihar daga cikin har da wanda ake zargi da hada abubuwan da ke fashewa da aka amfani da su a jihar.

Tuni dai rudunar ta rushe gidajen da aka gano makaman, kuma haka ta ce za ta ci gaba da yi.

Rudunar tsaron ta ce an tsananta sintiri da kuma tsaro a yayinda ake bukukuwan easter a jihar.

Karin bayani