Koriya ta arewa na shirin ko-ta-kwana

Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong-un ya umarci sojin kasar da su sanya makaman roka-roka cikin shirin ko ta kwana domin kai harin ga wuraren da Kasar Amurka ke da iko ko karfin fada a ji a yankin.

Wannan mataki dai ya biyo wani shawagin da wasu jiragen yakin Amurka su ka kai Koriya ta kud.

A baya dai Kin Jong-un ya umarci sojin kasar da su shiga cikin shirin ko ta kwana a yayinda ake ci gaba da zaman dar-dar a yankin.

Kafar yadda labarai mallakar gwamnatin Koriya ta arewa ta ce Shugaba, Kim Jog-un ya kira wani taron manyan kwamandojin sojin kasar domin tattauna shawagin da jiragen yankin Amurka su ka kawo yankin koriya din.

An dai ambato shugaban koriyar da cewa, muddin aka takali kasar, toh fa sojojin kasar za su kai hari a cikin Amurka da sansanin sojinta dake Guam a Hawaii da kuma Koriya ta kudu.

Ya ce shawagin da jiragen yakin Amurka biyu su kawo Koriya ta arewa wani mataki ne na tunzura Koriya ta Arewa.

Jiragen Yakin Amurka biyu sun taso ne daga jihar Missouri domin yin atisayen kai hari ta sama da yankin na Koriya a karo na farko.

Jiragen dai na iya daukar makaman nukiliya.

Wannan matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na cikin horon shekara-shekara da kasar ke gudanarwa a yankin a yayinda take ci gaba da fuskantar barazana daga Koriya ta Arewa.

A farkon wannan makon ma dai koriya ta arewa ta ce sojojinta a shirye su ke su kai hari duk inda dakarun Amurka su ke a yankin.