Mandela yana samun sauki a asibiti

mandela
Image caption Nelson Mandela yana murmurewa

Tsohon shugaban Africa ta Kudu Nelson Mandela ya shafe kwanansa na biyu a asibiti, inda ake yi masa magani akan cutar huhun da ta sake dawo masa.

Shugaban Africa ta Kudu, Jacob Zuma ya shaidawa BBC cewar, tsohon shugaban mai shekaru 94 a duniya, yana samun sauki.

Mista Zuma ya bukaci mutane kada su shiga cikin kaduwa, bayan an garzaya da Mista Mandela asibiti a daren Laraba.

A cewar Jacob Zuma, idan mutum wanda ya tsufa ya rasu, to bisa al'ada akan ce ya koma gida ne.