Sarakunan Arewa sun bukaci a yiwa 'yan Boko Haram afuwa

sultan
Image caption Sarki Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III

Majalisar sarakunan arewacin Najeriya ta koka game da yawan tashe-tashen hankulan da ake samu a yankin, inda ta bukaci gwamnatin tarayya ta dauki matakan zubar da jinin da ake fama da shi.

Sarakunan wadanda suka tattauna a fadar Sarki Musulmi dake Sakwatto, sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta duba yi wuwar sulhu da masu dauke da makamai, saboda ta hakanne kawai za a samu zaman lafiya a yankin.

Mai martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Najib Hussaini a hirarsa da BBC ya ce" ko ina a duniya ta hanyar sulhu ake magance tashin hankali, a don haka ya kamata gwamnati da duba lamarin".

Sarakunan Arewacin Najeriyar na ganin cewar ya kamata gwamnati ta sake duba batun afuwa ga masu dauke da makaman don kawo karshen tashe-tashen hankula.

Karin bayani